TSUMIN ƁAURE DON NI'IMA DA KASHE KWAYOYIN CUTA GA MATA YANADA MATUKAR AMFANI MACE TAKOYI WANNAN HADIN SOSAI
Wannan tsumi na musamman yana motsa sha'awa, ƙara ni'ima, da kuma kashe kwayoyin cuta a gaban mace.
Idan mace ta riƙa amfani da shi, zai taimaka mata wajen samun wadatacciyar ni'ima tare da kare ta daga matsalolin infection.
ABUBUWAN DA ZA,A NEMA:
✅ Sassaken Ɓaure
✅ Mazarkwaila
✅ Zuma
✅ Kananfari (a zuba mai yawa)
✅ Citta
YADDA ZA,A HADA:
1) A zuba sassaken ɓaure cikin tukunya, a ƙara ruwa mai yawa, sannan a dafa har sai ruwan ya kusa shanyewa.
2) A sauke, a tace ruwan, sannan a zuba zuma, mazarkwaila, kananfari, da citta.
3) A sake mayar da shi kan wuta ya tafasa na ɗan lokaci.
4) A sauke sannan a juye a cikin kwalba.
5) A riƙa shan kofi biyu safe da yamma.
AMFANIN WANNAN HADIN:
•Ƙara ni’ima da sanyin jiki
• Motsa sha’awa
• Kashe kwayoyin cuta da hana infection
• Taimakawa wajen gyaran jiki da farji
• Idan kika daure da wannan tsumi, za ki kasance cikin ƙoshin lafiya da wadatacciyar ni’ima.
🛑 Lura:
Idan kina da ciki, ki nemi shawarar likita kafin amfani da wannan hadin ko kuma kiyi hakuri kisauka lafiya saikiyi amfani dashi.
Idan kin sha kuma kin fuskanci wani canji mara kyau, ki dakata da amfani da shi.
Allah ya bada iko, ya kuma sa albarka! A raba da sauran ‘yan uwa mata domin amfana. Ameen.
0 Comments