YADDA AKEYIN ALALE KALOLI (10) NA ZAMANI MASU SAUKIN SARRAFAWA GA UWARGIDA DA AMARYA KU KARANTA ZAKU KARU SOSAI
01. ALALAN FULAWA
Abubuwan da ake buƙata:
* Fulawa
* Kwai
* Nama
* Kifi ɗanye
* Markaɗaɗɗen kayan miya
* Albasa
* Attarugu
* Curry
* Gishiri
* Maggi
Yadda ake haɗashi
- Da farko zaki tafasa Kifi sannan ki ɓare shi ki fidda tsokar.
- Bayan nan saiki kwaba fulawa da kauri kamar kwabin alala, fulawa gwangwani huɗu.
- Ki fasa kwai guda hudu akan fulawar da kika kwaɓa sannan ki zuba kifin da kika murmusa.
- Ki yanka nama ƙanana ki zuba a ciki sannan kuma ki zuba markaɗaɗɗen kayan miya ludayi ɗaya ki yanka albasa da attarugu, kisa curry, gishiri da maggi duk a ciki.
- Bayan nan kuma sai ki zuba mai gwangwani ɗaya ki juya sosai, ki shafa mai a gwangwanaye ki zuzzuba ko ki ƙulla a leda ki dafa shi.
02. ALALAN KABEJI
Abubuwan da ake buƙata:
* Kabeji
* Wake
* Hanta
* Kwai
* Kifi
* Attarugu da Albasa
* Maggi, Curry da Gishiri
* Manja ko Man gyada
Yadda ake haɗawa:
- Ki surfa wake gwangwani huɗu ki zuba attarugu da albasa a ciki sai a markada miki.
- Ki yanka kabejinki ƙanana mai ɗan yawa ki zuba akai, ki yanka dafaffen kwai kizuba akai, kisa maggi, curry, gishiri ki juya sosai, kisa mai gwangwani daya, ki kara juyawa ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa.
03. ALALAN DANKALI
Abubuwan da ake buƙata
* Dankali
* Nama
* Kwai
* Attarugu
* Albasa
* Curry
* Maggi
* Gishiri
* Mai
Yadda ake haɗashi
Ki dafa dankalinki ki marmasa ko ki daka, ki tafasa nama ki daka kizuba akai, ki jajjaga attarugu da albasa kizuba akai, kisa maggi, curry, gishiri da mai, ki fasa kwai kizuba akai ki juya sosai, ki zuba a leda ko gwangwani ki dafa.
04. ALALAN PLANTAIN (AGADA)
Abubuwan da ake buƙata
* Plantain
* Garin plantain
* Cray fish
* Dry fish
* Attarugu da Albasa
* Curry
* Manja
Yadda ake haɗashi
Ki bare plantain guda uku ko hudu, ki yanka kanana ki mutsittsike ko ki markada a blender, ki zuba garin plantain kofi daya da rabi akan plantain din dakika nika, ki gyara busasshen kifinki da dakakken cray fish akai, kisa maggi, gishiri, attarugu, albasa da mai akai ki juya, idan yayi kauri ki kara ruwa yazama kamar kullin alala, ki zuba a gwangwani ko leda ki dafa.
05. ALALAN DOYA
Abubuwan da ake buƙata
* Doya
* Nama
* Kwai
* Hanta
* Maggi da gishiri
* Currry
* Mai
Yadda ake haɗashi
Ki daka doyarki danya a turmi ko ki markada ta, ki markada danyan namanki, ki markada kayan miyarki ki zuba a kai, ki zuba maggi, gishiri da curry, ki zuba hantarki da kika yanka kanana, ki yanka dafaffen kwanki kanana, ki zuba kisa mai ki juya sosai, sai ki dinga zubawa a leda kina kullewa, ki zuba a tukunya ki zuba ruwa akai ki dafa minti ashirin ya dahu.
06. ALALAN KWAI, NAMA DA HANTA
7.
Abubuwan da ake buƙata
* Kwai
* Nama
* Hanta
* Albasa
* Attarugu
* Maggi da gishiri
* Curry
* Mai
Yadda ake haɗashi
Ki tafasa nama da hantarki da tafarnuwa da thyme da maggi da gishiri, ki yanka namar kanana, hantar kuma ki daka ta ki hada su guri daya, ki jajjaga albasa da attarugu ki zuba a kai ki fasa danyen kwai ki zuba akai, kisa maggi, gishiri, curry da mai ki juya sosai, ki zuba a leda ko gwangwani, ki dafa wannan alala yana gina jiki sosai.
07. ALALA DA MAI DA YAJI
Abubuwan da ake buƙata
* Wake
* Attarugu
* Albasa
* Maggi da gishiri
* Alayyahu
* Manja
YADDA AKE HADAWA
Ki wanke wake ki cire dusa ki zuba attarugu da albasa ki kai inji a markado miki, kisa maggi da gishiri ki juya sosai, ki shafa manja a gwangwanayenki ki dinga zuba kulli waken a gwangwanayen, idan kin zuba a tukunya ki turara, idan ya dahu sai ki juye a kwano ki zuba manja da yajin barkono akai.
08. ALALAN AGUSHI
Abubuwan da ake buƙata
* Agushi
* Wake
* Kifin gwangwani
* Hanta
* Attarugu
* Albasa
* Maggi da gishiri
* Curry da mai
YADDA AKE HADAWA
Ki sami wakenki gwangwani uku ki wanke ki fidda dusar, ki sami agushinki gwangwanin madarar ruwa daya ki soya, ki zuba waken, ki sami attarugu da albasa ki kai a markada miki, ki zuba kifin gwangwani guda biyu, ki zuba hantar ki, maggi, gishiri, curry da mai kadan, ki juya sosai, ki buga sosai, ki zuba kulla a leda ki dafa.
09. ALALEN DOYA
*doya
*kwai
*hanta
*maggi
*gishri
*curry
*mai
*albasa and attaruhu
*garlic idan kina so
YADDA AKE HADAWA
Dafarko zaki samu doyanki ki gurza a abun gurza kubewa sai kiyi blendng tare da attaruhu da albasa idan kin kammala sai kizo ki zuba spices dnki da mai ki dan buga kullun sai ki yanka dafaffen kwanki da hanta a cikin kulln ki kulla a leda ki dafa yanda ake dafa alale.
ki barshi ya dahu sosai sannan idan an gama sai servng ku gwada walh akwai dadi.
0 Comments