YADDA AKEYIN CHICKEN BALLS DA TAMARIN JUICE HADADDU NA ZAMANI MASU SAUKIN SARRAFAWA GA DADI
INGREDIENTS
kaxa
dankali
albasa
attarugu
kwai
mai
maggi
gishiri
Curry
YANDA ZAKI HADA SHINE
A dafa kaxa da kayan kamshi da dandano tayi taushi sosai a cire iya tsokar a ajiyeta a kwano sai a dafa dankali a dagargaxashi a kan kaxar , sai kiyanka albasa da attaruhu akai ki murmusa maggi akai kixuba curry kifasa kwai ki kada ki ajiye sai kiringa mulmula hadin kaxar nan kina sawa a ruwan kwai kina soyawa.
YADDA AKEYIN TAMARING JUICE HADADDE
Kayan hadi
•Tsamiya
•Suger
•Kanunfari
•Citta
•leman tsami
YADDA AKE HADAWA
dafa suger da ruwa barshi ya huce.dafa tsamiya da ruwa,kanunfari da citta har misalin minti 30.
tace tsamiyar abarshi ya huce yayi sanyi.
matse leman tsami a kuma yanka guda biyu
yankan fadi.
hada dafaffan suger acikin tsamiya zuba leman tsami da kuma wanda aka yanka a cikin jug.asaka cikin frig(Refrigerator) yayi sanyi sosai kafin sha.
zaki zuba ruwa dai dai tsamin dakakeso kafin sha.
0 Comments