YADDA AKEYIN FREID YAM WITH EGG HADADDE NA ZAMANI TARE DA MIYAR DA ZA'ACI DA ITA
INGREDIENTS
*Doya*
*Kwai*
*Maggi*
*Gishiri*
*Citta*
*Mai*
Kayan dandano da kukeso
YADDA ZAKU SARRAFASHI
Dafarko xaki dafa doya kisa pillar kiyi slicing dinta saiki fasa kwai kisa maggi albasa da yar citta kadan sai ki kada sannan ki xuba wannan doyar akai,saiki dora frying pan ki xuba mai kadan dayayi xafi sai ki xuba hadin doyar kadan kamar dai yadda kike soya kwai, a haka har ki gama.zaki iyaci da yar gajeriyar miya ko kici haka
YADDA ZAKU HADA MIYAR DA ZA'ACI
Tumatirin gwangwani
*Albasa*
*Attaruhu*
*Mai*
*Maggi*
*Kayan dandano*
Zaki dora tukunya akan wuta kixuba ruwa kadan idan yayi xafi sai ki xuba tumatirin gwangwani aciki ki gauraya xaki ga y y dan kauri sai ki xuba maggi, mai,gishiri, da jajjagen attaruhu da tattasai sai albasa enough kisaka aciki ki juya sai ki rufe ki barsu su dahu.
intayi xakiga miyar tayi dan kauri kadan yadda dai xaki iya cin doyar da ita.
idan kina bukatar kifi ko Nama xaki iya anfani dasu shikenan girki ya kammala muhadu cikin Wani girkin nagaba inshAllah
~By @Chef Oum Aslam Kitchen✍🏻~
0 Comments