YADDA AKEYIN KUNUN AYA HADADDE SPECIAL NA ZAMANI MAI DADIN GASKE
INGREDIENTS:
Aya
Dabino
Kwakwa
Madarar gari
Ginger
Kananfari
Vanilla ko coconut and banana
YADDA AKE HADAWA
Dafarko zaki samu aya mai kyau sai ki jikata tunda safe ko kuma a kwara mata ruwan
Zafi abarta tayi 30min, sai a surfata a turmi acire kasa da dattiin jikinta.
Idan an surfa sai a wanketa tas asa ginger da kananfari da dibino amma sai an cire kwallayon an wanke, da kwakwa itama sai an fere bakin bayan sai ayanka kanana sai akai a markada ko a markada a bulanda.
Idan an markada sai a tace asa madara da sugar da flavour agauraya sai asa a fridge ko asa kankara akwai Flavours din KUNUN AYA ynxu masu dadi saikiyi amfani dashi
Note : idan kunun ayan ya kwana yana baci ya lalace saiyayi iri saikiyi dai-dai Amfanin Lokacin.
0 Comments