INGREDIENTS
Wake kofi 3
Maggi
Gishiri
Kayan kamshi
Man gyada
Attarugu
Albasa
Tattasai
YADDA AKE HADAWA
Da farko uwargida za ki wanke wakenki ki cire hancin ya fita tas.
sai ki zuba attarugu da tattasai, sai ki yanka albasa ki bayar a kai markade.
Idan ankawo sai ki zuba maggi da gishiri da kayan kamshi.
Sai ki dauko ludayi mai kyau babba sai ki ta bugawa, ya bugu sosai.
Anan sai ki dora manki a wuta. Idan ya yi zafi, sai ki sa karamin ludayinki ki na diba ki na sawa a manki kadan kadan har ki gama, ammafa ki
tabbatar ki nayi ki na bugawa.
Za’a iya ci da kunu ko koko ko daima shayi.
NOTE:- Wani sirri yin KOSAI yayi kyau sosai ba,asamai Wani kalan maggi kwantawa zaiyi bazeyi yadda akesoba
Da,ankawo mk nika farin maggi da gishiri kawai zakisa kibuga kisoyashi.
KUNUN GYADA MAI AYABA HADADDE NA ZAMANI
INGREDIENTS
Gyada
Ayaba
Gero
Sugar
madara
YANDA AKEYI:
Zaki gyara gyadarki kisoyata sama sama kiwanketa kisamu manyan ayabarki ki maikyau ki markadesu kidora akan wuta kibarta dahu idantafara fitarda kumfa kidauko garin nikakkiyar gyadarki 2tbspn kixuba acikin kunun gyadar ki kawo kullun kamu na gero kamar 3spn kidamashi da ruwa kizuba akai zakiga yagame jikinshi yadanyi kauri kisauke idan yakisha kizuba sugar da madara Shikenan ya kammala sai sha.
0 Comments