Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN KUNUN MADARA HADADDE MAI DADI

         YADDA AKEYIN KUNUN MADARA HADADDE MAI DADI UWARGIDA ADINGA                         CANZA TUKUNYA



INGREDIENTS 

Couscous na kunukofi daya da rabi Madarar gari kofi shida Ruwa babban kofin shan ruwa biyu da rabi Coconut milk kofi daya Ruwan kwakwa rabin kofi Flour (don daure kunun) Sugar yadda ake bukata.


               YADDA AKE HADAWA

Ki samu tukunya ki dora akan wuta ki sa ruwa ba dayawa ba ki sa sugar idan ruwan ya yi zafi sai ki sa couscous, ki bashi kamar minti takwas ya nuna kada ki bari ya fara fashewa. Ki samu roba ki sa milk na ki ki dama da ruwa, ki sa coconut milk, coconut water ki juya su hade sai ki sa 2½ cup na ruwa ki sake mixing.


Bayan 8 minutes din sai ki zuba mixture na ki a cikin tukunyar ki juya. Ki bari ya yi tashi kaman sau biyu. Ki samu karamin roba ki sa flour sai ruwa kadan ki dama ki tace, sai ki sa akan kunun don ya danyi kauri. Sai ki sauke bayan minti daya.


Karin bayani Za ki iya shan kunun madara da zafinsa ko kuma za ki iya sa a fridge in ya yi sanyi ki sha. 


Idan ki ka sake daura kunun madara akan wuta dan ya dumamu zai salamce



        

        

Post a Comment

0 Comments