ALAMOMIN RASHIN JINI DA KUMA ABUBUWAN DA SUKE KAWOSHI TARE DA SAMUN MAFITA GA MATSALAR
Anemia(cutar rashin Jini) yanayi ne dake faruwa sakamakon rashin samun isassun wasu sinadaran jini masu lafiya don ɗaukar iskar oxygen zuwa sassan jiki. Samun anemia (Rashin jini)na iya sa ka ji gajiya da kasala.
Akwai nau'o'in cutar anemia da yawa, kowanne da dalilinsa. Rashin jini shine mafi yawan sanadin cutar anemia.
Anemia na iya zama na ɗan lokaci ko na dogon lokaci, kuma yana iya kamawa daga mai sauƙi zuwa mai tsanani.
Ana iya magance cutar Rashin jini (anemia) daga shan magunguna kafin aje ga karin jini.
Cin nau'ukan lafiyayyun abinci na taimakawa wurin hana kamuwa da wasu nau'ukan cutar anemia.
ALAMOMIN RASHIN JINI (anemia)
sun bambanta dangane da dalilin da yajawo shi amma yana iya haɗawa da:
-Gajiya
-Rashin karfin jiki
-Saurin bugun zuciya
-karancin numfashi
-Ciwon kirji
-hajijiya
-hasken fatar jiki
-kunburin jiki (yana farawa da fiska)
-Matsalolin fahimta
-Sanyin hannaye da ƙafafu
-Ciwon kai
Anemia na iya zama mai sauƙi, kuma ba lalle a gane shi ba. Amma alamun suna karuwa yayin da abun ke tsananta.
DALILAN DAKE JAWO RASHIN JINI (ANEMIA)
Anemia yana faruwa ne lokacin da aka rasa sinadaran dake tafiyar da iskar oxygen a cikin jinin. Wannan na iya faruwa idan Jikin mutum baya sarrafa isassun wadannan sinadarai (red blood cells) da sauri fiye da yadda za a iya maye gurbinsu.
Wadanda Sukafi Shiga Hatsarin Kamuwa da Rashin Jini
-mace me ciki
-yara kanana
-wanda suka samu zubar da jini da yawa lokacin al'ada
-masu sikila
barin cuta tadau lokaci me tsawo ta yanda zata hana jiki sarrafa ko zukar (absorbing) na sinadarin iron da vitamins dasauran su.
Da zaran anji alamu da aka zayyana asama ayi kokarin tuntubar masana ko garzayawa zuwa asibiti domin fadada bincike
Allah yakara mana lafiya.
0 Comments