YADDA AKE HADA SABULUN GYARAN FATA GA AMARE DA BAKAR MACE DA KUMA FARAR MACE
ANA BUKATAR ABUBUWA KAMAR HAKA:
Sabulun Diyana
Sabulun Salo
Lalle
Majigi
Zuma
Garin Darbejiya
Dawa’ussabuni
Sabulun Premier Antiseptic
Kurkum
Sabulun Zaitun
Dudu Osun
Dettol
Yadda Ake Hada Sabulun:
1. A daka sabulun duka sai a zuba su a container.
2. A ƙara lalle, majigi, zuma, da kurkum sannan a haɗa su sosai.
3. Garin darbejiya kuma za a shanya ganyenta a daka, a tace, sannan a zuba a ciki.
4. A saka ruwa kaɗan a gauraya har ya haɗe jikinsa sosai.
Fa'ida:
Za ki ga fatarki ta canja, sirrin kyaun jikinki zai bayyana. Sai an gwada, za a tantance!
Gyaran Jiki da Fuska – Domin Laushi da Sheki
Za ki tanadi kayan haɗi kamar haka:
1. Man Zaitun
2. Lalle
3. Kurkum
4. Madarar ruwa (Peak)
Yadda Ake Amfani:
A haɗa su wuri guda, a kwaba, sannan a shafe jiki da fuska.
A jira ya bushe, sai a murje, sannan a shiga wanka.
Fa'ida:
Hadin nan yana sa jiki yayi kyau da sheki in sha Allahu.
Hadin Dalleliya – Domin Gyaran Jiki da Fuska
Za,a tanadi:
1. Kurkum
2. Dilka
3. Zuma
4. Kwai
5. Lemon Tsami
Yadda Ake Amfani:
A haɗa su wuri guda, sai a samu ruwa a kwaba kamar yadda ake kwaba lalle.
Sai a shafa a fuska da jiki, bayan awa 1, sai a shiga wanka.
Fa'ida:
Jiki zai goge, fuska za ta yi haske da annuri. Wannan shi ake kira Dalleliya.
Hadin Gyaran Fata Na Musamman (Amare Sun Fi Yin Sa)
Za a tanadi:
1. Lalle
2. Kwaiduwar kwai 3
3. Manja (Cokali 3)
4. Kurkum
Yadda Ake Amfani:
A kwaba su wuri guda, a shafa a jiki tsawon awa 1.
A yi wanka da ruwa zalla, sai a jika duka da ruwan dumi a shafa a jiki, sannan a yi wanka.
Fa'ida:
Yana sa fata ta zama laushi da shauki.
Gyaran Fuska – Don Haske da Lafiya
Za a tanadi:
1. Dettol
2. Sabulun Ghana
3. Garin Zogale
4. Farar Albasa
Yadda Ake Amfani:
A haɗa su wuri guda, a kurɓa su a turin fuska sannan a mulmula.
A riƙa wanke fuska da su akai-akai.
Fa'ida:
Yana sa fuska ta yi kyau, ta zama sumul, kuma yana magance kuraje.
Hadin Gyaran Fuska da Jiki – Don Haske da Sumulci
Za a tanadi:
Bawon Kankana
Yadda Ake Amfani:
A riƙa goge fuska da bawon kankana.
Fa'ida:
Yana gyara fata, yana sa fuska ta zama sumul da laushi.
Hadin Gyaran Jiki Na Musamman – Domin Laushi da Damshi
Za a tanadi:
1. Ayaba
2. Lemon Tsami
3. Tataciyar Madara
4. Kwai (Farin Kwaya 1)
YADDA AKE AMFANI:
1. A markada ayaba a blender ko a matse da hannu.
2. A ƙara tataciyar madara da fari kawai na kwai.
3. A matse lemon tsami, a haɗa su gaba ɗaya.
4. A shafa a jiki na tsawon awa 1, sannan a yi wanka da ruwan ɗumi.
Fa'ida:
Yana sa fata ta zama laushi, tare da ɗaukar kyau da walwali na musamman.
✅ Idan aka lazimta wannan hadi na kwana 3, za a sha mamaki!
0 Comments